'Yan awanni bayan an kashe wasu mutane guda uku a garin Ancha da ke karamar hukumar Bassa a jihar Plateau. An sake kashe wasu mutane bakwai kuma aka kone gawakinsu a makwabtan kauyen Hukku a karamar hukumar ta Bassa.
Kakakin kungiyar ci gaban matasa Miango mai suma Mr. Lawrence Zongo ne ya tabbatar da kisan mutanen wanda aka aikata ranar Alhamis.
Ya kara da cewa maharan sun fi 200, sun kuma kone gidaje fiye da 23 na kauyawan sakamakon harin da suka kai da sanyin safiyar Alhamis.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari