Duba cututtuka guda 10 da abarba ke magani a jikin dan Adam

Legit Hausa
Kayan marmari su na da matukar amfani ga jikin Dan Adam
Daga cikin masu irin wannan amfani akwai Abarba
Abarbara na gina jiki kuma yana maganin cututtuka da dama
Musamman ma ta fuskar kare jiki daga kamuwa da ciwon zuciya, abarba na daya daga cikin 'ya'yan itatuwa masu amfani a jikin dan adam.
Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam a sanadiyar arzikin wasu muhimman sunadarai da ta kunsa kamar su; fibres, minerals, calcium, manganese, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.
Wadannan sinadarai da abarba ta kunsa na taka muhimmiyar rawar gani wajen amfani ga rayuwar dan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.
Ga jerin cututtuka da kuma illoli da dama da abarba ke magancewa a jikin dan Adam:
1. Cutar Arthritis: Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai sanya rikewar gabbai da jijiyoyi inda su ke kumbura har su hana mutum sakat.
2. Cutar Daji (Cancer): Abarba na maganin cutar ‘kansa’ mai lahanta kwayoyin garkuwa saboda sinadarin da ta kunsa na vitamin A da C da sauran su.
3. Sanyi da mura: Yawaita shan abarba na bayar da kariya daga cututtuka na mura da sanyi domin kuwa tana kunshe da wasu sinadarai da ke kashe majina.
4. Karfin hakori: Kadan daga aikin Abarba akwai kara karfin jijiyoyin hakori ta kuma kara lafiyar dasashi da kare hakora daga cututtuka. Tana kuma kara lafiya da gyara suma watau gashi na jikin mutum.
5. Karfin gani: Haka kuma abarba na kara kaifin idanu don haka mai shan abarba zai dade da idanun sa garau ko ya tsufa.
6. Hawan jini: Abarba na kare cutar hawan jini saboda sindarin Pottasium da take dauke da shi mai amfani wajen yawo da jini a jikin mutum.
7. Abarba na hana tsufa: Abarba ta tsaya ga gyaran idanu kadai ba yayin da tsufa ya cimma mutum domin kuwa tana kare mutum daga cutar dimuwa, mantau da sauran cututtuka na tsufa.
8. Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage daskararren maiko wato cholesterol a jiki.
9. Tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da tashin zuciya. Tana maganin tsutsar ciki da saukaka fitar bahaya.
10. Abarba tana inganta garkuwar jiki, lafiya da kare shi daga cututtuka.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN