Masallata a kasar Pakistan sun yi arangama da jami'an 'yansanda da suka je domin ganin sun hana yin Sallan Juma'a sakamakon dokar hana cinkoson jama'a saboda matsalar cutar coronavirus.
Arangaman ya faru ne a wajen wani Masallacin Juma'a inda aka gan wani faifen bidiyo inda jama'a suka dinga jifan jami'an tsaro, kuma suka yi wa motocinsu biyu luguden duwatsu.
Kasashen Pakistan, Bangladesh da India, sun yi ta lallashin malaman addinai domin su fadakar da mabiyansu kan muhimmancin hana cinkoson jama'a domoin ganin an dakile yaduwaar cutar coronavirus.
A yankin Sindh na kasar Pakistan , an sanya dokar hana cinkoson jama'a daga karfe 12 zuwa karfe 3 na rana, amma lamarin ya gamu da cikas a kasa da take da yawan mutum 2,708 da suka kamu da cutar.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari