1. TSAIDA BUGUN ZUCIYA:- bugun zuciya shike gyara dumin
jiki da daidaita numfashi to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika
raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan film na kasar indiya
da yan ball da boxing da wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu
kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine
yake jawo musu..
.
2. LALATA TSARIN KAYAN CIKI:- shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji
guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo
matsalar hanji ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan
ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar
ciki
.
3. DAUKE KARFIN JIKI:- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji
dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayinda
ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai naurorin jikin sunyi kokarinsu
na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin hakan yanasa
suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. Ko kun lura duk
sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman
farkon zazxabi a hankali kuma sai kuji ya daina.?
.
4. CIWON MAKOGWARO DA DAKUSHEWAR MURYA:- Yawan amfani da ruwan sanyi
yana lalata jijiyoyin makogwaro har sukai ga basa amfaninsu mai kyau a
mai sha yakai shekaru arbain sai ya fara fama da ciwon makogwaro da
dakushewar murya ko muryar ta fashe kwatankwacin mashayin taba
.
5.CIWON HANTA DA KODA:- dukansu suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu
don haka yayinda bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su
kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa in haka ta samu mutum ya
shiga matsala
.
6. BUSAR DA RUWAN JIKI:- akwai naurori a jikin dan adam da aikinsu shine
sadar da ruwa ko ina a jikin mutum ta yanda ko ina na jikinsa zai samu
damar motsawa cikin nishadi. To wadannan naurorin sukan yi sanyi
sakamakon ruwan sanyi sai su zama so weak
.
7. MATSALAR MAAURATA:- Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani
cewa shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji yana kuma busar da
mace in mahaifarta nada rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka
maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali ko kuma ya rage masa kuzari.
Yana dauke niimar jiki su zamo basa gamsuwa da juna
.
8. BASIR DA CIWON KAI NA GEFE MIGRAINE:- shan ruwan sanyi yanda nace
muku yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya
hadu da basir.
Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa migraine.
Shi kuma migraine yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai in yayi
nisa har hauka yana sawa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari