Ga kadan daga cikin munanan illoli da ke tattare da tsaka.
1.
Idan aka bar kowane irin garin abinci a bude, ta kan shiga tayi birgima a
cikin garin. Bayan an tuka wannan garin, yawanci an kamu da cutan
barasu wato kuturta ko wasu mugayen kuraje
2. Idan aka bar ruwan sha a bude sai tayi amai a cikin ruwan bayan ta
sha ruwan. Yawanci sai ka ga an kamu da shanyewan jiki wato paralyze ko
kuma lallacewar sassan jiki.
3. Idan mutum ya kwanta bacci bai yi
addu’a ba, ta kanye busa a cikin idon mutum. sai ka ga yawanci an samu
lalacewar gani mai kyau ko a makanshe.
4. Idan tsaka ta rika, misalin ire-iren gobara da ta ke faruwa a yanzu
so da dama tsaka ce amma bamu sane ba, domin ita tsaka tana tare da
mugayen jinnu. Dama Fiyayyen Halitta Ya ce, ita ce tayi busa ga wutan da
aka jefa Annabi Ibrahim (A.S).
5. An ta samu labarin wata mata da ta tafasa ruwan shayi da tsaka a
cikin butan shayin, a sanadiyar wannnan tsakar ita da mijin ta, da yaran
suduk suka bakunci lahira.
Kadan kenan daga cikin ilolin tsaka
saboda haka mu kula da ita wannan dabba wadda ta ke mu’amala a cikin
gidajen mu, mi kula da abincin mu da abun shan mu, domin mu kauracewa
wannnan illar da wannan dabba.
Idan mun gan ta a cikin gida, a yi kokarin kashe ta kuma a anbace sunan
Allah (S.W.T) domin tana
tare da shaidanu don tana cutar da mutane.
*A yi amfani fa tsintsiya,
*ko takalmi wajen kashe ta
*ko kuma a sa mata maganin kashe kwari
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari