Yansanda sun kama kasurgumin Dan fashi a matattarar yan wiwi

Rahotun Legit Hausa

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami daya fitini al’ummar yankin Ikorodu na jahar. Daily Trust ta ruwaito yansanda sun kama Sanni Abiodun inkiya Abbey Boy ne a wani samame da suka kai wata matattarar yan wiwi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

Rahotanni sun ce an kama Abiodun ne a mashayar yan wiwin dake titin Araromi dake Igbogbo, inda Yansandan suka binciko wasu makamai tare da buhunan wiwi a wurin. Mataimakin sufetan Yansandan shiyya ta 2,

AIG Ahmed Iliyasu ne ya bayyana haka yayin da yake bajekolin dan fashin a babban ofishin Yansandan shiyyar. Iliyasu yace sun kai samamen ne bayan samun koke-koken jama’a game miyagun ayyukan Abbey da yaransa a yankin, don haka ya umarci hazikin Dansanda, Uba Adams ya kamo shi.

AIG Iliyasu yace bayan sun yi ma Abbey tambayoyi, ya amsa laifinsa, kuma ya tabbatar da mallakar bindigar da aka gani a wajensa da alburusai, wanda yace da su yake amfani a fashi.

Da ya sha matsa, Abbey ya bayyana sunan wani mutumi Babajide a matsayin maigidansu, wanda yace shi ne ya kawo masa tabar wiwin da aka kama domin ya sayar masa. Daga karshe Iliyasu yace tuni sun kaddamar da farautar Babajide don tabbatar da sun kama shi, sa’annan yace zasu gurfanar da Abbey gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kansa.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ba za ta lamunci harin da yan bindiga suke kai a jahar Katsina ba, don haka ya yi alkawarin daukan mataki.

Daily Trust ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne biyo bayan mummunan harin da yan bindiga suka kai a kananan hukumomi uku, inda suka kashe mutane 47, tare da jikkata wasu da dama. Buhari ta bakin kakaakakinsa, Garba Shehu ya ce ba za su bari harin ya wuce haka nan ba har sai sun rama biki da harin ramuwar gayya, wanda yayi daidai da tsarinsa na kare jama’an kasa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post