Covid-19: Zanga-zanga ta barke ta nuna rashin goyon baya kan dokar takaita zirga-zirga

Rahotun Legit Hausa

Babu shakka gwamnatocin kasashe da dama na ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar annobar coronavirus wadda ta yiwa duniya lullubi.

A yunkurin haka gwamnatocin kasashe da dama na Turai da kuma na nan gida a nahiyyar Afirka, sun dauki matakin shimfidawa al'ummomin su dokar tilasta zaman gida. Da yawa daga cikin gwamnatocin sun yaba wa al'ummomin su sanadiyar yiwa wannan doka da'a da kuma samun hadin kansu na dakile yaduwar cutar.

Sai dai wani rahoto da muka samu daga sashen Hausa na BBC dangane da ababen da ke faruwa a jamhuriyyar Nijar ya sha ban-ban da sauran kasashe. Mun ji cewa zanga-zanga ta barke a jamhuriyyar Nijar ta nuna rashin goyon baya a kan dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin kasar ta shimfida saboda annobar coronavirus.

Rahotanni sun bayyana cewa, matasa a birnin Yamai da ke jamhuriyyar Nijar sun bazama wajen gudanar da zanga-zanga ta nuna rashin amincewa da dokar gwamnati ta hana zirga-zirga. Gwamnatin Nijar ta shimfida dokar hana fita wadda ta ke fara aiki daga karfe 7.00 na Yammaci zuwa 6.00 na safiyar kowace rana.

Har ta a daren ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu, matasan Yamai sun cinna wuta a unguwanni bakwai, lamarin da ya janyo jami'an tsaro suka yi musu tarnaki da barkonon tsohuwa. Rashin nuna goyon baya ya sanya matasan suka bijire wa dokar hana fita da gwamnatin ta shimfida, inda suke ci gaba da karade tituna tare da kona tayoyi da lalata ababen more rayuwa.

Lamarin bai takaita a nan kadai ba domin kuwa mashaida sun tabbatar da cewa matasan bayan zanga-zanga sun kuma koma far wa dukiyoyin al'umma. Legit.ng ta fahimci cewa, masu fada a ji da kuma hangen nesa musamman iyaye da kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun yi Alla-wadai da wannan lamari.

Sun kuma kirayi matasan a kan yi wa dokar gwamnatin kasar biyayya wadda ta shimfida da zummar dakile yaduwar cutar coronavirus.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN