Rahotun Legit Hausa
A lokacin azumin watan Ramadan, yana da matukar muhimmanci
mutum ya ci abinci mai gina jiki sannan ya sha ruwa ko ababen sha domin gusar
da kishi yayin sahur da bayan bude baki. Kishin ruwa yana iya janyo mutuwar
jiki, bushewar labba, kishi da ciwon kai.
Hakan yasa ya ke da muhimmanci mutum ya rika shan ruwa da
abubuwa masu dauke da ruwa a lokacin azumi.
Duk da cewa mai azumi ba zai sha ruwa ba har sai faduwar
rana, akwai wasu matakai da zai dauka domin rage kishin ruwa mai tsanani.
1 - Guji shan ababen sha masu dauke da caffeine: Caffeine
wani sinadari ne da ke cikin ganyen shayi, coffee da sauransu kuma yana sanya
yawan fitsari wanda hakan ke fitar da ruwa da gishiri daga jikin dan Adam. Shan
caffeine mai yawa zai sanya kishi sosai saboda haka zai fi dacewa mutum ya sha
ruwa ko kuma kayan itatuwa yayin sahur da bude baki.
2 - Ka bude baki da kayan marmari da ganyaye: Baya ga iganta
lafiya da kayan itatuwa da ganyaye keyi, suna kuma taimakawa wurin magance
kishi saboda jikin dan adam ya kan sarrafa su a hankali ne wanda hakan zai sa
ba za aji kishi da wuri ba bayan cin kayan marmari da ganyaye.
3 - Guji yawan gishiri da yaji: Gishiri da yaji da kayan
kamshi na girki suna kara sanya kishi saboda haka idan mutum zai yi girki sai
da takaita gishiri, yaji da kayan kamshi.
4 - A rika yin wanka da ruwan sanyi: Yin wanka da ruwan
sanyi a lokacin watan Ramadan yana taimakawa mutum wurin rage jin kishin ruwa.
Yin wankan yana rage zafin jikin mutum wanda hakan na nufin ba zai yi gumi
sosai ba ya zubar da ruwan jikinsa.
5 - Guji kwalkwalan ruwa mai yawa cikin kankanin lokaci:
Shan ruwa mai yawa lokaci guda ya kan sanya mutum ya yi saurin fitsarar da
ruwan saboda haka ya fi dacewa mutum ya rika shan ruwan kadan-kadan bayan an
bude baki.
6 - Takaita shiga rana ko wuri mai zafi sosai: Yana da
wahala mai azumi ya kauracewa shiga rana ko wuri mai zafi baki daya amma yana
kyau ayi kokarin kauracewa tsananin zafi. Zafi ya kan sanya gumi wanda hakan ke
janyo kishin ruwa. Mutum ya rage yawo cikin rana ya rika zama a inuwa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari