Duba abin da wasu matasa suka yi da sunan Ministan shari'a a jihar Kebbi

Kungiyar Khadi Malami Matasa Progressive Association tare da hadin guiwa da Abubakar Malami For Governor (AMG) 2023, sun gudanar da aikin feshin maganin sauro a garin Birnin kebbi.

An fara aikin feshin ne daga Shataletalen Sarki Yahaya zuwa Shataletalen sabuwar Kasuwa, kuma aka ci gaba da wannan aiki wanda Malam Habibu Bello ya dauki nauyi.

Shugaban kungiyar matasa na Khadi Malami Matasa Association Malam Habibu Bello, ya ce " Wannan taron matasa ne na Birnin kebbi Lgt suka hada kungiya don su tallafa wa mai girma Minista kan wannan tafiya tashi, saboda irin kokari da yake yi.

Za mu yi feshin maganin sauri a cikin karamar hukumar Birnin kebbi daga wannan shataletale, shiyar Sarakuna da shiyar Junju. Shi ya sa muka kira manyan mu domin su zo su sa hannu mu fara wannan aiki".

'"Kuma za mu ci gaba da sa lokacin mu da kudinmu, za mu bayar saboda wannan tafiya ta mai girma Minista ta yi amfani ga jama'ar jihar Kebbi gaba daya ba karamar hukumar Birninj kebbi ba kawai".

Alhaji Nasiru Turakin Masama, wanda shi ne shugaban kungiyar AMG mai karadin ganin Abubakar Malami SAN, ya zama Gwamnan jihar Kebbi 2023, ya ce " Muna matukar farin ciki da wannan tsari da matasan karamar hukumar Birnin kebbi suka yi. Muna fatan duk matasan kananan hukumomi 21 su yi koyi da wannan kungiya, kuma idan Allah ya yarda, wannan sako naku zai isa ga mai girma Minista.

"Idan Allah ya yarda kungiyarmu ta AMG tare da mai girma Minista, za mu shigo ciki, domin ganin irin gudunmuwa da za a baku. Wannan abu da kuka yi ya yi daidai da manufofin Minista, na taimaka wa mutane, wajen aikin rogo, samar da ruwan sha, da sauransu.

Ku yi kokari ku hada sunayenku tare da kuma masu neman a yi masu aiki, kamar aikin famfo dasauransu, a tura zuwa ofis na mai girma Minista in Allah ya yarda zai taimaka maku".

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN