Buratai ya koma yankin Arewa maso gabas na kasar nan don jagorantar yakar Boko Haram

Rahotun Legit Hausa

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya koma yankin Arewa maso gabas din kasar nan don jagoràntar yaki da 'yan ta'adda. Legit.ng ta ruwaito hakan ne bayan takardar da daraktan hulda da jama'a na rundunar,

Kanal Sagir Musa, ta fita a ranar Juma'a, 10 ga watan Afirilu. A yayin jawabi ga dakarun da ke sansanin Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga ta jihar Borno, Buratai ya ce zai kasance tare dasu duk rintsi da tsanani.

Kamar yadda takardar ta bayyana, shugaban rundunar yana yankin Arewa maso gabas din tun a ranar 4 ga watan Afirilu don zagaya wuraren da dakarun suke. Takardar ta kara bayyana cewa, a yayin zagayen, ya samu damar zantawa da manyan hafsoshin sojin tare da rundunoni.

 "Rundunar sojin Najeriya na shaidawa 'yan Najeriya cewa ta mayar da hankali wajen kare 'yan kasa tare da rayukansu. "Akwai bukatar jama'a su san cewa babu wani kalubalen tsaro da ya gagara. Boko Haram da ISWAP sun kusa zama tarihi", takardar tace.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta dauka tsauraran matakai don ganin bayan mayakan Boko Haram. Ya sanar da hakan ne a fadar shugaban kasa a Abuja yayin da ya karba bakuncin Gwamna Babagana Zulum na jihar Yobe a ranar Alhamis.

An yi taron ne bayan aikin da dakarun kasar Chadi suka yi a yankin tafkin Chadi bayan an halaka musu sojoji 100. Buhari ya ce wadannan matakan sun zama dole a daukesu don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da ci gaba a yankunan da Boko Haram suka yada zango a Najeriya.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN