Gaskiyar abin da ya kamata ka sani game da fasahar sadarwa ta 5G

Rahotun Jaridar Aminiya


Cece-kucen da ake ta yi a kan fasahar sadarwa ta 5G ya kara zafafa a ‘yan kwanakin nan, bayan da wasu suka danganta lamarin da cutar coronavirus.

Tuni dai wasu masana harkar sadarwa suka alakanta wannan cece-kuce da gasa a tsakanin Amurka da China, wadda ke kan gaba a wajen samar da sabuwar fasahar.

Aminiya ta zanta da masanin harkar sadarwa Yunusa Zakari Ya’u, wanda ake yiwa lakabi da Y.Z. Ya’u. wanda ya karyata ikirarin da ke danganta fasahar da annobar COVID-19.

A cewarsa, fasahar ta 5G wadda ke da karfi kuma za ta samar da damar aika sakwanni cikin hanzari fiye da wadanda suka gabace ta, wato 4G da kuma 3G, ba za ta rasa illar tururin radiation wanda ido ba ya gani ba, kamar ko wace na’ura mai kwakwalwa.

Ya ce sauran takwarorin wannan fasaha da suka gabace ta ma, duk suna samar da wannan tururi.Sai dai a cewarsa dukkan na’urori masu kwakwalwa da a ke kirkirowa, a kan yi nazari a kansu tare da tabbatar da sahihancin lafiyarsu ga al’umma, gabanin kera su a matakin sayarwa.

“Ko ita kanta wannan waya da muke magana da kai ta hanyarta a yanzu, ai tana
fitar da tururin.

“Sai dai abin da ke faruwa shi ne, dole ne a tabbatar da adadin da ke fita daga jikinta bai kai mataki mai illtarwa ba.

“Kuma ai wannan shi ne aikin hukumomin da ke kula da al’amuran sadarwa, irin tamu a nan Najeriya, wato Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta NCC.

“Ko a lokacin da aka fara amfani da wayar hannu ta GSM, ai an yi ta yin irin wannan batu.
“To haka lamarin yake a duk lokacin da wata sabuwar fasahar sadarwa za ta fito.

“Wannan Magana ta son zuciya da ake yi, cewa na’urar 5G ce ta jawo annobar COVID-19, ta faro ne daga kasar Amurka, sannan ta bazama zuwa Turai; sai a yanzu ne ta iso kasashenmu”.

Sai dai kuma a cewar masanin, wannan magana ba gaskiya ba ce.

“A kimiyyance ba gaskiya ba ne, farfaganda ce kawai ta abokan hamayya.

“Ita Amurka tana cikin kasashen da ke yin aiki a kan samar da fasahar, sai kasar China ta yi wa dukkan kasashen zarra a kai”, inji shi.

Y.Z. Ya’u ya bukaci jama’a da su fahimci cewa; “Ba wata fasahar sadarwa ta zamani da ba ta da illa, sai dai akan tabbatar da cewa an samar mata da hanyar kariya, gabanin a ba da lasisin fitar da inta”, inji shi.

“Sannan a san cewa, duk wata sabuwar fasaha da za ta shigo kasar nan sai an tantance ta, tare da ba da lasisi a kai.

“Kuma ina jin a kan wannan matakin ne ake game da fasahar ta 5G a hukumar NCC—ba a kai ga ba da lasisi a kai ba”, inji masanin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN