• Labaran yau


  'Yansanda sun halaka mai garkuwa da mutane, sun kwace tarin makamai

  Rundunar yansandan jihat Rivers ta tabbatar da halaka kusurgumin mai satar mutane domin garkuwa da su  Samuel Naakpo, wanda ya dade yana addabar jama'ar da ke yamma maso gabacin hanyar Ogoni zuwa Uyo.

  Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Nnamdi Omoni ya sanar da haka, ya kuma ce an yi nassarar halaka Samuel ne bayan wani bayanin sirri da jami'an suka samu. Sakamakon haka suka je mabuyarsa amma ya arce da gudu, lamari da ya sa yansanda suka bindige shi a karamar hukumar Ogu-Bola.

  An sami tarin makamai da albarussai da suka hada da bindigu kirar GMP No NN 07150, da  G-3.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yansanda sun halaka mai garkuwa da mutane, sun kwace tarin makamai Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama