'Dansanda ya karya hannun Likita wajen aiwatar da dokan zama a gida don coronavirus

An rage wa sajen na 'yansanda mukami zuwa Kofur bayan an same shi da laifin duka tare da raunata wani Likita a jihar Akwa Ibom.

Dan sandan mai suna  Edidiong Alexander ya raunata Dr Daniel Edet wanda Likitan fida ne, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki ne a Assibitin koyarwa na Uyo, yayin da dan sandan ya tsayar da shi daga bisani aka sami matsala da ya kai ga dansandan ya dake shi har ya karya masa hannu ranar Juma'a da yamma garin aiwatar da dokar zama a gida saboda cutar coronavirus.

Kungiyar Likitoci ta Najeriya Nigerian Medical Association ta yi barazanar shiga yajin aiki kan lamarin, sakamokon haka hukumar 'yansanda ta jihar Akwa Ibon ta hukunta dansandan, bayan ta same shi da laifin tuhuma da aka yi masa, sai ta rage masa mukami daga Sajen zuwa Kofur.

Kwamishinan 'yansandan jihar Imohimi Edgal , ya kai ziyara wajen Likitan da dansandan ya raunata, ya kuma ba shi hakuri tare da kungiyar Likitoci na Najeriya.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN