• Labaran yau


  COVID-19: Yansanda sun kwace babur da ya dauko mata da diyarta mara lafiya zuwa asibiti

  Yansanda a kasar Uganda sun kwace babur daga wani mai suna Joseph Muwanga yayin da ya dauko wata mata mai suna Magdalene Namazzi tare da diyarta karama mara lafiya lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Asibiti.

  Amma hotuna da suka bayyana sun nuna yadda Magdalene Namazzi ta gurfana ta dukufa tana rokon yansandan cewa kada su kwace babur daga wajen Joseph, domin ba da gangan ya karya dokar hana fita  ba.

  Ta ce tafiya da babur zuwa  Asibiti ne  hanya mafi sauki da sauri domin ceton ran karamar yarinyar.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: COVID-19: Yansanda sun kwace babur da ya dauko mata da diyarta mara lafiya zuwa asibiti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama