Covid-19: An kori yansanda 2 daga aiki bayan sun yi ma wata mata dukan tsiya

An yi wa yansanda biyu da aka nuna a faifen bidiyo suna dukan wata mata a garin Iwo na jihar Osun koran kare daga aikin dansanda.

Wadanda aka kora daga aiki su ne  Inspector Ikuesan Taiwo mai lambar aiki AP NO 251724 da PC Abass Ibrahim mai lambar aiki No. 509634.

Matar da yansandan suka yi wa duka mai suna Tola Azeez, ta fito ne daga gida domin ta saye magani saboda wani danuwanta baya da lafiya, amma sai yansanda suka yi mata dan karen duka wai ta karya dokar hana zirga zirga don cutar coronavirus.

Babban safeton yansandan Najeriya Adamu Muhammed ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike bayan ya ga bidiyon yadda yansandan suka yi wa matar duka.

Rahotanni sun nuna cewa bayan kora da aka yi wa tsoffin yansandan  daga aiki, za a kuma gurfanar da su a gaban Kotu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN