• Labaran yau


  An sami karin mutum 114 da suka kamu da cutar coronaavirus cikin awa 24 a Najeriya

  An sami karin mutum 114 da suka kamu da cutar coronaavirus a cikin awa  24 da suka gabata wanda adadin wadanda suka kamu dacutar a Najeriya ya kai 1095.

  A wani kididdiga  da cibiyar kula da manyan cutuka na Najeriya NCDC ta fitar, ta ce 80 daga cikin adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar an same su ne a jihar Lagos..

  Sai kuma 21 a Gombe, 5 a birnin tarayya Abuja, 2 a Zamfara, 2 a jihar Edo, 1 a jihar Ogun, I a jihar Oyo, 1 a jihar Kaduna sai kuma 1 a jihar Sokoto.

  A daidai karfe 11:30 na  dare ranar 24 ga watan Aprilu an tabbatar da adadin mutum 1095 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, an sallami mutum 208 yayin da mutum 32 suka mutu.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An sami karin mutum 114 da suka kamu da cutar coronaavirus cikin awa 24 a Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama