• Labaran yau


  COVID-19: An kama yansanda da suka yi wa mata duka bayan ta fito domin ta sayi magani

  An kama wasu yansanda da suka bayyana a wani faifen bidiyo da suke dukan wata mata da ta fito domin ta saya wa yanuwanta magani a jihar Osun.

  Kama yansandan ya biyo bayan umarnin Safeto janar na yansanda ne Muhammed Adamu.

  Adamu ya ce hukumar yansanda ba za ta lamunci cin zali da rashin bin dokokin aikin dansanda ba daga kowane jami'inta.

  Wadanda aka kama kuma suna fuskantar bincike da shari'ar yansanda da ake kira Orderly room, sun hada da Safeto Ikuesan Taiwo mai lambar aiki AP NO 251724 da PC Abass Ibrahim mai lambar aiki No. 509634

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: COVID-19: An kama yansanda da suka yi wa mata duka bayan ta fito domin ta sayi magani Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama