COVID-19: Gwamnatin Gombe ta haramta sallar jam’i

Rahotun jaridar Aminiya
Gwamnatin jihar Gombe ta haramta sallar jam’i da ma dukkan tarurrukan da suka kai na mutum biyu zuwa sama bayan da ta ayyana dokat hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 na safe.
Wannan mataki dai, wanda kuma ya hada da umarnin rufe dukkan kasuwannin jihar ban da na magani da abinci, ya biyo bayan samun wasu mutane da aka tabbatar suna dauke da cutar coronavirus.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ta gidajen rediyoyin jihar bayan kammala wani taro da suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da na hukumomin tsaron jihar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kara da cewa dokar zaman gidan za ta fara aiki ne daga karfe 6 na yammacin ranar Alhamis.
Ya ce duk wata harkar saye da sayarwa da ta kunshi mutane biyu an haramta ta saboda gudun yaduwar cutar ta coronavirus sannan ya karfafa cewa dole mutane su dinga nisantar juna da yawaita wanke hannu.
Duk wata kasuwa a jihar an rufe ba mu yarda a bude kowacce irin kasuwa ba sai ta magani da kayan abinci”, inji gwamnan.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma ce duk wata makarantar tsangaya dole a rufe ta sannan almajiran da ba ’yan asalin jihar ba ne malamansu su gaggauta mayar da su garuruwan su na asali don kauce wa fushin hukuma.
Har ila yau dokar ta yi tsananin da hatta zirga-zirga daga wata karamar hukuma zuwa wata an dakatar sai da wani kwakkwaran dalili kuma da izinin Kwamitin Ko-ta-kwana a kan Yaki da cutar ta coronavirus.
Ranar Talata ne dai aka tabbatar da samu mutane biyar wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus a jihar Gombe.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN