Mai Martaba Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan Azumin Ramadan

Rahotun BBC Hausa

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin jinjiirn Watan Ramadan a Najeriya. 

Sarkin Musulmin ne ya ce an ga jinjirin watan na Ramadana a daren Alhamis, inda ya ce Alhamis 23 ga watan Afirlun 2020 ce ranar karshe ta watan Sha'aban na Shekarar Hijira ta 1441.
Sannan ya ce Juma'a 24 ga watan Afrilun 2020 ce ranar farko ta watan Ramadana na Shekarar Hijira ta 1441.

"'Yan uwa al'ummar Musulmi, bisa ga sharuddan Musulunci, muna sanar da ku cewa yau Alhamis 29 ga watan Sha'aban shekara ta 1441 bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 23 ga watan Afrilun shekarar 2020, an kawo karshen watan Sha'aban na shekara ta 1441," in ji Sarkin Musulmi.

"Mun samu tabbacin ganin Watan Ramadan daga kungiyoyi da shugabannin Musulmi daga ko'ina a cikin kasar nan, kuma kwamitocin tantance ganin wata na kasa da na jihohi sun tantance kuma mun tabbatar."

Kamar Najeriya, haka ma kasashen Musulmai da dama, da suka hada da Saudiyya sun sanar da ganin Watan Ramadana din a ranar Alhamis.

A wannan karon dai al'ummar Musulman duniya za su fara azumin ne cikin dokar kulle sakamakon annobar cutar korona da ake kokarin dakile yaduwarta.

Yawanci duk shekara, batun ganin watan Ramadan na janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya sannan ana yawan samun sabanin fara azumi tsakanin Najeriya da makwabciyarta Nijar.

Azumin watan Ramadana na daya da cikin shika-shikan Musulunci. Ana kwashe kwanaki ashirin da tara ko talatin ana yin azumin.

Kuma Musulmi kan kaurace wa ci da sha da kuma saduwa da iyali daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Ramadana wata ne mai alfarma da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga Mahalicci.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN