Buhuri ya aika sako na musamman ga Musulmin Najeriya dangane da cutar coronavirus

Rahotun Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ja hankalin daukacin musulman duniya, a kan kada su mai da annobar korona uzirin da zai hanasu azumi a cikin watan Ramadana. Buhari ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yake taya musulman duniya murnar shigowar watan azumi, tare da fatan alkhairi a gare su.

Sai dai Buhari ya gargadi masu azumin da su takaita al'adun cakuduwa da aka saba lokacin azumin watan Ramadana kamar yayin sallolin dare na Asham da Tahajjud. Ya kuma gargadi al'umma a kan kauracewa shiga taron jama'a, lamarin da ya ce kada kwadayin neman lada ya sanya su jefa kawunansu ga hadarin kamuwa da cutar korona.

A yayin da yake jan hankali shugaban kasar ya nemi al'umma da su ci gaba da dabi'ar bayar da tazara a yayin da mahukuntan lafiya ke fafutikar dakile yaduwar annobar cutar a fadin duniya. Ya tunatar da al'ummar Najeriya a kan dauka izina da shawarwarin da gwamnatocin kasashen duniya suka bayar a yayin gudanar da ibadu cikin wannan wata mai albarka.

Ya nemi kowane musulmi da su rika buda baki da sahur tare da gudanar da sauran ibadu a killace daga su sai iyalansu a cikin gidajensu. Hakika kwararrun lafiya na duniya sun shawarci dukkanin al'umma a kan yawaita ta'ammali da kayan abinci da na sha masu bunkasar garkuwar jiki yayin da likafar cutar korona ke ci gaba.

A halin yanzu dai an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 27 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbata Taskar bayanai ta NCDC a ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 981 yayin da mutum 197 suka samu waraka. Ya zuwa yanzu dai mutane 31 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda bayanan alkaluman NCDC suka tabbatar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN