Covid-19: Duba sakon gaggawa da Ganduje ya aika wa dakunan gwaji a jihar Kano

Rahotun Legit Hausa

Cibiyar kula da ma'aikatun lafiya ta kudi ta jihar Kano ta bada sanarwar cewa asibitoci 300 na kudi a jihar Kano ne za su iya aiki amma iyakar abinda suka yi rijista. Cibiyar ta shawarci dakunan gwaji da ke jihar da su daina aiki na wannan lokacin.

Cibiyar ta kara da jan kunne asibitocin kudin cewa za ta iya rufe su matukar basu da kayan kariya na ma'aikatan lafiya. Sakataren cibiyar, Dr Usman Eti ya sanar da jaridar The Punch a ranar Juma'a cewa wannan dokar na daga cikin umarnin gwamnatin jihar ga masu cibiyoyin lafiya na kudi.

Hakan ce hanya daya da za ta takaita yaduwar cutar ga ma'aikatan lafiya na cibiyoyi masu zaman kansu. Eti ya ce, "An kiyaye wannan umarnin ne tun daga kungiyar likitoci ta Najeriya, kungiyar ma'aikatan jinya da ungo-zoma da kuma kungiyar masu hada magani ta kasa.

"Duk cibiyoyin killacewa masu zaman kansu da suka mallaki kayayyakin kariya na ma'aikatan lafiya za su iya aiki. "Ba mu fatan abinda ya faru a jihar Legas ya maimaita kansa a nan. Dole ne mu kiyaye."

Ya kara da cewa, "An shawarci dukkan dakunan gwaji masu zaman kansu da su rufe tare da daina aiki." Kamar yadda yace, cibiyar tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da kwamitin yaki da cutar na jihar za su saka ido a kan hakan. Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa a ranar Alhamis ta ce mutum 73 ne suke dauke da cutar COVID-19 a jihar Kano.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN