Bayan mahaifiyar yaron ta kula da wasu halaye da bata saba gani ba a wajen 'danta, sai ta yi bincike, kuma yaron ya shaida mata abin da Abdullahi ke yi dashi.
Sakamakon haka ta shaida wa mahaifin yaron, wanda daga bisani ya kai kara a ofishin NSCDC.
Kakakin hukumar NSCDC na jihar Jigawa Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar 13 ga watan Aprilu a ofishin hukumar da ke Dutse.
Ya ce " Sakamakon gwaji daga babban asibitin Dutse ya nuna cewa an yi luwadi da yaron, amma babu kwayoyin cuta da ake iyadaukawa ta hanyar jima'i".
Ya ce wanda ake zargi da aikata laifin ya shaida wa jami'an NSCDC cewa " Nikan bukaci yaron ya raka ni mu je gona ne wanda ke daga wajen gari, a nan ne nike aikata wannan lamari da shi"
Adamu ya ce rundunar NSCDC na jihar Jigaawa za ta gurfanar da Abdullahi a gaban kuliya manta sabo na Majistare da zarar sun kammala bincike.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari