Duba sharudda da IMF ta gindaya wa Najeriya kafin a bata tallafin dala biliyan $3.4bn

Rahotun Legit Hausa

Asusun lamunin duniya IMF ya amince da baiwa gwamnatin Najeriya tallafin $3.4bn (N1.2 tiriliyan) domin yakar muguwar cuta mai toshe numfashi Coronavirus (COVID-19). A ranar Talata ne dai kwamitin zartarwa na Asusun Lamunin ya amince da bukatar kasar Najeriya bayan da ta nemi tallafin kudi na Dalar Amurka biliyan 3.4

Wannan tallafi da asusun lamunin ya baiwa Najeriya shi ne mafi yawa da zai baiwa wata kasa a duniya kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito. Asusun lamunin na bada tallafin mai suna 'Rapid Financing Instrument (RFI)' ne ga kasashe mambobin kungiyar amma babu su a cikin kowane irin shirin taimako na IMF.

Sabanin yadda wasu ke hange, ko kadan wannan kudi da Najeriya ta karba ba rance bane. Tsarin gudanarwa na IMF ya bai wa wasu kasashe damar ajiye wani kaso na lalitar dukiyarsu a Asusun. Ana rike wadannan ajiya cikin kudin da ake kira SDR (hakkin zarar kudi na musamman). Darajar SDR ta dogara ne a kan darajar kudin wasu kasashen duniya ciki har da na Amurka,

Turai, Birtaniya, Japan da kuma na kasar Sin. Dala biliyan 3.4 da Najeriya ta samu a yanzu yana wakiltar SDR 2,454.5 miliyan kenan, kaso 100% na adadin kudin da Najeriya ke rike da su a IMF. Sai dai IMF na bari kasashe su zari wannan kudi domin saduwa da bukatun gaggawa kama daga aukuwar bala'o'i, barkewar rikici, tashin farashin kayayyaki da kuma sauran bukatu yayin da kasa ta fuskanci rauni.

Kasancewarta mamba a IMF, dole ne Najeriya ta sake dawo da wannan ajiya cikin asusun na IMF. Haka kuma dole ne Najeriya ta gina wannan ajiyar a Asusun Lamunin cikin lokacin da bai wuce shekaru 3 zuwa 5 ba. IMF na bayar da irin wannan taimako ga kasashen da su ke fuskantar matsalolin kudi.

A cikin sanarwar bayar da lamunin da ya fitar a ranar Talata, IMF ya ce a shirye ya ke ya bayar da shawarwari kan manufofin yadda Najeriya za ta batar da wannan kudi. IMF ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta bayyana duk wani shige da fice da za ta yi yayin kashe kudaden. A halin yanzu dai wannan kudi da Najeriya za ta karba ba zai magance matsalolinta ba, domin kuwa tana ci gaba da neman dala biliyan 3.5 daga bankin duniya da kuma bankin ci gaban Afirka (AfDB)

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN