Ibtila'in Luwadi a Birnin kebbi: Yara 3 yan shekara 10 sun bayyana a Kotu

Wasu yara guda uku yan kimanin shekara 10 kowanensu, sun bayyana a gaban Kotun Shari'a ta Nassarawa 1 a garin Birnin kebbi bisa tuhumar aikata Luwadi tsakaninsu.

Bayan yaran da muka boye sunayensu, sun bayyana suka zauna a kan benci da ke gaban Alkali, sai suka yi shiru, mai gabatar da kara ya bukaci su gaya wa Alkali dalili da ya sa aka kawo su Kotu.

Duk da haka yaran sun kasa cewa uffan, daga bisani Alkali ya ce "Idan baku gaya mana gaskiya ba zan sa a yi maku bulala".  Daga bisani daya daga cikin yaron ya ce " Mun je mu ci munta ne" watau sun je domin su aikata Luwadi ne.

Alkali ya tambaye su cewa " Wa ya koya maku wannan mugun aiki?" Sai daya daga cikin yaran ya ce wani ne da ake kira Naziru, wanda ke zaune a unguwar Bayan Tasha a garin Birnin kebbi.

Yaron ya kara da cewa " Yana bamu Naira hamsin N50 ne,sai ya yi mana a kwarkwada".

Alkali Mu'awiya Shehu Birnin kebbi, ya bayar da umarnin cewa a nemo Naziru kuma a kama shi a yi cikakken bincike kan lamarin. Daga bisani ya bayar da umarnin cewa a kai yaran gidan gyara halinka na yara (Remand Home) ha ranar 12/3/2020 kafin a dawo da su Kotu.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN