Dan sandamai gabatar da kara Cpl. Faruk Muhammed mai lambar aiki 493010, ya shaida wa Kotu cewa ranar 3/3/20202 Abubakar ya sa Hijabin mata, ya shiga gidan Aliyu Hakimi da ke garin Asarara, da niyyar aikata zina da matarsa Hauwa'u Aliyu.
Mujallar ISYAKU.COM ya gano cewa Abubakar ya ci karo da rashin sa'a, domin Allah ya tona masa asiri.
Bayan mai gabatar da kara ya karanta wa Abubakar laifin da ake tuhumarsa a gaban Kotu, Abubakar ya ce " Abin da ake tuhuma na dashi gaskiya ne".
Sakamakon haka, Alkali Mu'awiya Shehu Birnin kebbi, ya bayar da umarnin a kai Abubakar Kurkuku zuwa mako daya domin a yanke masa hukunci.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari