Hotunan kwarto da ya shiga gidan matan aure da hijabi a kauyen Asarara jihar Kebbi

Wata Kotun Shari'a ta Nassarawa 1 a garin Birnin kebbi, ta tasa keyar wani matashi mai suna Abubakar Garba zuwa Kurkuku, bayan ya amsa laifin shiga gidan wata matar aure da niyyar ya aikata zina da ita a garin Asarara da ke jihar Kebbi.

Dan sandamai gabatar da kara Cpl. Faruk Muhammed mai lambar aiki 493010, ya shaida wa Kotu cewa ranar 3/3/20202 Abubakar ya sa Hijabin mata, ya shiga gidan Aliyu Hakimi da ke garin Asarara, da niyyar aikata zina da matarsa Hauwa'u Aliyu.

Mujallar ISYAKU.COM ya gano cewa Abubakar ya ci karo da rashin sa'a, domin Allah ya tona masa asiri.

Bayan mai gabatar da kara ya karanta wa Abubakar laifin da ake tuhumarsa a gaban Kotu, Abubakar ya ce " Abin da ake tuhuma na dashi gaskiya ne".

Sakamakon haka, Alkali Mu'awiya Shehu Birnin kebbi, ya bayar da umarnin a kai Abubakar Kurkuku zuwa mako daya domin a yanke masa hukunci.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN