Type Here to Get Search Results !

'Yar aji SS2 ta rasu bayan zargin duka daga malamin makarantarsu a jihar Katsina

Wata yarinya mai suna Fatima 'yar ajin SS2 a makarantar Sakandaren Arabiyya na Gwamnati a garin Fago jihar Katsina, ta mutu sakamakon zargin cewa Malaminsu wanda ke karantar da lissafi mai suna Abubakar Suleiman ya yi mata bulala .

Daily Trust ta ruwaito cewa, Abubakar Suleiman ba hakikanin Malami bane, ko dan kwangilan koyarwa a Makarantar, amma shugaban Makarantar ce ta dauko shi bisa tsari na kashin kanta domin ya koyar da dalibai akan N5000 kowane wata.

Hakazalika Daily Trust ta ce, Mahaifin yarinyar Maikano, ya ce ya sami sakon cewa diyarshi bata da lafiya, sakamakon haka ya samo wasu yan uwansa suka je Makarantar, kuma aka shaida masu cewa Fatima ta yanke jiki ta fadi bayan ta fito daga dakin wanka, kuma ana zaton cewa Iskoki ne suka shafe ta.

Sakamakon haka, Mahaifin Fatima ya dauke ta ya kaita Asibitin Gwamnati a garin Daura, inda Likita ya tabbatar da rasuwar Fatima.ranar 13 ga watan Fabrairu.

Kwana hudu bayan rasuwar Fatima, Mahaifinta ya je ya karbo jaka da sauraan littafan Fatima daga Makarantar.

Lokacin da yake duba takardunta, sai ya ci karo da wani Kundi watau Diary, inda dalibai ke rubuta ababen da suka faru da su a kullum a cikin Makaranta. Sai ya ci karo da inda Mariganya Fatima ta rubuta da hannunta cewa:

“Allah Sarki ranar Alhamis munzo firef akaci miyi lilin muka yi malam Abu sikitu ya bugimu har ya fasni ko ma goshi banda lafia ina masassara da ciwon baya kamar na mutu”

Sakamakon haka Mahaifin Fatima ya koma Makarantar inda ya shaida wa shugaban Makarantar Principal Fatima Yakubu abin da ya gani a takardar da Maringanya Fatima ta rubuta.

Sakamakon haka lamarin ya kai ga Ma'aikatar ilimi na jihar Katsina, inda suke ci gaba da gudanar da bincike, yayin da wata majiya ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, an dauke Prinsipal na Makarantar an dawo da ita Ma'aikatar ilimi , aka kuma bata takardar neman ta yi bayani bisa tuhuma da Ma'aikatar ke yi mata a kan rashin kulawa kamar yadda ya kamata.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN