Type Here to Get Search Results !

Zan iya hada mijina da karuwa, na san zai iya gundura da ni kadai - Budurwa

Rahotun Legit Hausa
Wata budurwar Najeriya tayi ikirarin cewa ba ta damu ba idan mijinta na neman mata barkatai. Kamar yadda ta wallafa, babu dadi mutum ya nace cin abu daya a kowacce rana. A kalla da namiji na bukatar abinci kala-kala. Idan kuwa haka gaskiya ne, toh tabbas ba zai so mace daya ba.
Kamar yadda Funke Fatai ta bayyana, da kanta za ta samowa mijinta wasu karuwan don ya ji dadin rayuwar shi ta duniya.
Zan iya hada mijina da karuwa, na san zai iya gundura da ni kadai - Budurwa
“Ina daga cikin matan da ba zasu gallaza wa mijinsu ta hanyar cewa sai ni kadai zai kwanta da ni ba. Ni ko saurayi ne muke tare, na kan hada shi da wata kawata wacce na amince da ita ya kwanta don jin dadin rayuwar shi.
“Shinkafa na da dadi amma akwai wasu lokuta da za ki ba namiji dama ya mori taliya ko tuwo.”Ta ce.
Wannan wallafar kuwa ta jawo mata caccaka daga bakin mata masu miji da kuma wadanda basu da mijin. Wasu na ganin cewa don dai ba aure tayi bane kuma ba ta san ciwon zama da miji ba balle ta amince mishi da bin karuwai.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN