Rahotun Legit Hausa
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya ce Muhammadu Sanusi II , tuɓaɓɓen Sarkin Kano yana da 'yancin tafiya ko wane gari har da Kano.
Bayan cire shi daga sarauta, akwai rahotanni da ke yaɗuwa na cewa ba shi da izinin shiga Kano na a ƙalla watanni uku. Amma yayin amsa tambayoyin manema labarai a garin Awe a jihar Nassarawa, gwamnan na ya ce kotun babban birnin tarayya ta yanke hukuncin cewa Sanusi yana da ikon tafiya duk inda ya ke so.
El-Rufai ya ce, "Babban kotun ta yanke hukuncin cewa yana da 'yancin zuwa duk inda ya ke so, har da Kano amma ina tunanin yana son ya tafi Legas domin ya tarar da iyalansa."
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN