Sarki Sanusi II ya samu ‘yanci zai bar garin Awe
Tubabben Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu ‘yanci a yanzu haka yana shirin fita daga garin Awe da ke jihar Nasarawa.
An dai kai tubabben Sarkin Kano, garin Awe ne don zaman hijira bayan Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tube shi daga gadon sarauta.
Rahotanni daga jihar Nasarawa sun ce Sanusi II ya gabatar da Sallar Juma’a a garin Awe kamar yadda mutanen garin suka bukata.
A yayin ziyarar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, rahoton na cewa Gwamnan da Sanusi II za su tafi Abuja inda daga nan zai kama hanyar zuwa Legas.
Hakan dai ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotu a Abuja ta bayar na cewa a bai wa Muhammadu Sanusi damar shiga ko ina a Najeriya ban da Kano.
Kotu ta abayar da umarnin a saki Sarki Sanusi
Wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin a saki tubabben Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da ke zaman hijira garin Awe a jihar Nasarawa.
Mai shari’a Anwuli Chikere, ne ya sanar da hakan ranar Juma’a, bayan shigar da karar da lauyoyin Sanusi II, suka yi gaban kotun wanda Alkali Lateef Fagbemi (SAN ) ke jagoranta.
Kotun ta sanar da ranar 26 ga Maris 2020, don ci gaba da sauraran shari’ar.
Kotu ta kuma umarci Sufeton Janar ‘yan Sandan Najeriya da shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS da sauran masu hannu a tsare tsohon Sarki Muhammadu Sunusi na II da su sake shi.
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da sarakunan Lafiya da Awe sun ziyarci tubabben Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II a garin Awe.
Gwamnan ya isa Awe ne da missalin karfe 5:10 na yammacin yau Alhamis tare da Sarkin Lafiya inda suka ziyarci tsohon sarkin a masaukin baki na Shugaban Karamar Hukumar Awe inda Sanusi yake zaune bayan tube shi daga sarautada Gwamnatin Jihar Kano ta yi a ranar Litinin.
Sarkin Awe ya isa gidan tun karfe 5:10 don tarbar Gwamna Sule.
Ziyarar Gwamnan ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa cewa an dauke tsohon Sarkin Kanon daga Awe.
Sai dai Aminiya ba ta samu bayani kana bin da Gwamnan da sarakunan suka tattauna da Sanusi II ba.
Rahotun Jaridar Aminiya
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN