Rahotun Jaridar Aminiya
Wani mutum mai shekaru 35 mai suna Habeeb Kasali, ya shiga
komar ‘yan sandan jihar Ogun bisa zargin da ake masa na kashe wani mutum
mai suna Bamidele Johnson, wanda ya ce yana badala da matarsa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola
Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa jami’an sun kame mutumin wanda ya
tsere bayan ya aikata aika-aikar,”
‘Yan uwan mamacin sun shigar da
maganar ga rundunar ‘yan sanda, inda suka ce fada ne ya barke a tsakanin
wanda ake zargin da mamacin mai shekaru 32, wanda ake zargi da kisan ya
hau shi da fada yana fada masa cewa, yana badala ta matarsa duk da cewa
a baya ya yi masa kashedi ba sau daya ba, ba sau biyu ba, daga nan ya
sanya almakashi ya soki mamacin a kirji da ido da wasu sassan jikinsa,
lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa a asibitin Crest da ke yankin Egan a
Legas.” In ji shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun CP Kenneth Ebrimson, ya bada
umarnin tura wanda ake zargin sashin binciken manyan laifuka na rundunar
domin ci gaba da bincike a yayin da ake ajiye da gawar mamacin a dakin
ajiyar gawa na babban asibitin Sango Ota a Jihar Ogun.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari