• Labaran yau


  Abubuwa 5 da duniya ta fuskanta cikin wannan shekarar ta 2020

  Rahotun Legit Hausa

  Cikin kimanin kwanaki 75 da kwashe cikin sabuwar shekarar 2020, alummar duniya sun fuskanci akalla jarabawa biyar da basu taba gani ba ko ji a tarihi ba ko kuma an dade ba a yi ba Akalla mutane 13000 sun mutu a fadin duniya, anyi asarar amfanin gona, yanayin rayuwar mutane ya sauya, tsoro da fargaba ta mamaye zukatan mutane.

  Ga jerin abubuwan

  01. Annobar Coronavirus Shiga sabuwar shekara ke da wuya, wata sabuwar kwayar cuta ta bayyana a kasar Sin wacce ke kama mutane cikin kankanin lokaci. Bayan watanni biyu da bullar cutar, mutane 276,000 suka kamu da ita, 13,000 sun mutu sakamakonta kuma 83,968 sun warke. Cutar ta bulla a kasashe akalla 180 a duniya wanda ya hada da Amurka, Ingila, Jamus, Faransa, Saudiyya, Rasha, da sauransu.

  02. Miliyoyin fari da dangwaye sun cika kasar Yamen da wasu kasashe a gabashin Afrika Wasu fari sun bayyana a kasashen gabashin Afrika irinsu Habasha dss inda suke hallaka kayan gona. An siffata farin a matsayin mafi hadari a tarihi kuma sun shiga kasashe irinsu Somaliya, Habasha, Sudan, Djibouti, Eriteriya, kuma akwai yiwuwan sun karasa kasar Uganda.

  03. Rikicin addini a kasar Indiya Rikicin addini ya barke a kasar Indiya tsakanin Mabiyar Hindu da Musulai inda aka kashe akalla mutaen 43, yawanci Musulmai, a gaban jamian tsaro tamkar da hannun gwamnati. Rikicin ya samo asali ne bayan majalisar dokokin kasar ta samar da sabuwar dokar hana Musulmai shigo kasar Indiya da kuma zama yan kasa. Hakan bai yiwa Musulman kasar, har da wasu da ba Musulmai dadi ba.

  04. Girgizan kasa a kasar Turkiyya Mutane 41 sun hallaka yayinda 1,600 sun jikkata a gabashin kasar Turkiyya bayan girgizan kasa a ranar 24 ga Junairu, 2020. Abin ya kai ga kasashen makwaftan Turkiyya irinsu Armeniya, Syiria da Iran sun girgiza.

  05. Fashewar bututun gas a Legas Najeriya An samu fashewar iskar gas ranar 15 ga Maris inda akalla mutane 17 suka rasa rayukansu kuma 15 suka jikkata a karamar hukumar Abule Ado ta jihar Legas. Gidajen akalla 50 sun kone kuma anyi asarar miliyoyin dukiya.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Abubuwa 5 da duniya ta fuskanta cikin wannan shekarar ta 2020 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama