• Labaran yau


  Wata matar aure ta kashe mijinta da wuka kan zargin yana lalata da wata a titi

  Rahotun Legit Hausa

  An tabbatar da mutuwar wani mutumi bayan matar shi ta caka masa wuka bayan wata rigima ta hada su a gidansu dake jihar Rivers yankin kudancin Najeriya Wani mai amfani da shafin kafar sadarwa na Facebook mai suna Anthony Biko Shadrach ya wallafa cewa matar dan uwanshi ta kashe shi da wuka saboda ta gano yana lalata da wata.

  Ya ce: "Yanzu yanzu, duniyar nan ta zama abin tsoro, dan uwana ya rasa ransa sanadiyyar caka masa wuka da matarsa tayi. A wani martani da ya mayarwa da daya daga cikin abokanansa mai suna Kaandy, wanda yace ya jiyo maganganu da yawa akan wannan lamari na dan uwan nasa, Anthony ya kara da cewa:

   "Kawai wata 'yar karamar hatsaniya ce ta hado su da matarshi, koda ace yana zuwa yana lalata da wata ne ma bai kamata ta dauki rayuwarshi ba. Ana ta samun matsaloli tsakanin mata da miji a Najeriya dake kai ga daya ya dauki makami ya kashe daya duk kuwa da cewa kotu na hukunci akan duk wanda aka kama da hannu a irin wannan ta'asa.

  A kwanakin baya dai babbar kotun Abuja ta yanke hukunci akan Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta akan zargin yana da wata budurwar a titi. Wannan hukunci na ta ya tada hankalin mutane da yawa a Najeriya musamman mata, sannan kuma ya jawo kace nace matuka a kasar ta Najeriya.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wata matar aure ta kashe mijinta da wuka kan zargin yana lalata da wata a titi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama