• Labaran yau


  Fiye da gidaje 100 sun lalace bayan tashin ababen fashe fashe a wata mota a jihar kudu

  An sami fashe fashen ababe da ya yi sanadin lalata fiye da gidaje 100 a garin Eleyowo da ke karamar hukuma Akure ta arewa a jihar Ondo.

  Mazauna garin sun ce an sami fashe fashen ne da safiyar ranar Asabar 28 ga watan Maris, lamari da ya katse zirga zirga tsakanin Akure zuwa Owo, kuma ana fargaban mutane da dama sun sami rauni.

  Wannan ya faru ne kasa da kilomita daya daga filin saukan Jiragen sama na Akure, lamari da ya bata wani Mujami'a, da wata makaranta tare da gidajen bayin Allah.
  Sai dai Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya ce lamarin ya faru ne bayan mota da take dauke da ababen fashe fashen ta sami matsala yayin da take dauke da kayakin fashe fashen na jami'an tsaro zuwa makwabciyuar jihar.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Fiye da gidaje 100 sun lalace bayan tashin ababen fashe fashe a wata mota a jihar kudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama