Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai ya kamu da cutar Coronavirus

Rahotun Legit Hausa

Mai girma Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya shaidawa Duniya cewa ya na cikin wadanda cutar nan ta COVID-19 ta kama a halin yanzu.

Kwamishinan harkar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da wannan a shafinsa na Tuwita da kimanin karfe 8:10 na daren Asabar. Mista Samuel Aruwan ya fitar da cikakken jawabin da Mai girma gwamnan jihar ya yi, bayan ta tabbata ya kamu da wannan cuta ta Coronavirus.

Gwamnan ya bayyana cewa gwajin da ya yi, ya nuna cewa ya na dauke da kwayar COVID-19. Gwamnan ya ce a halin yanzu ya killace kansa. Sai dai duk da haka ya yi kira ga jama’a su bi dokoki da sharudan da aka gindaya domin hana yaduwar cutar ta Coronavirus da ta addabi kasashe.

Ga abin da jawabin ya ke cewa: “Jawabin Malam Nasir El-Rufai game da sakamakon gwajin cutar COVID-19 da ya yi a Ranar 28 ga Watan Maris 2020. A cikin farkon makon nan, na mika jinina domin ayi mani gwajin COVID-19. Sakamako ya fito da yamman nan, kuma ina mai takaicin sanar da ku cewa, gwaji ya nuna ina dauke da cutar.

Kamar yadda hukumar NDDC ta tanadi kula da wanda bai fara nuna alamun cutar COVID-19 ba, na kebe kaina daga jama’a. Ina so in roki nutanen jihar Kaduna su cigaba da daukan matakan rigakafin da aka riga aka sanar.

Ya na da matukar muhimmanci ga kowa ya yi bakin kokari, ta tsaya a cikin gida domin ya kare lafiyarsa. Mataimakin gwamna ta na jagorantar kwamitinmu da ke yaki da cutar COVID-19, kuma za ta cigaba da fitar da bayani lokaci bayan lokaci. Nasir Ahmad El-Rufai 28 ga Maris, 2020”

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN