Wani mutum ya kashe makwabcinsa dattijo a kan batan wayar hannu

Rahotun Legit Hausa

Wani matashi mai shekaru 27 a jihar Ogun ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar. Ejike Okata ya yi sanadiyyar mutuwar makwabcinsa mai suna Obalende ne da ke Ijebu-Ode a jihar. A wata takardar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya halaka makwabcinsa mai shekaru 50.

Kamar yadda Oyeyemi ya sanar, "ya sassara makwabcinsa da adda a kan karamar hayaniya kuma wanda ake zargin ya tsere tun bayan aukuwar lamarin." Ya yi bayanin cewa, an kama Okata ne bayan rahoton da wani kaninsa ya kai wa 'yan sandan Obalende a ranar 28 ga watan Fabrairun 2020.

 "Bayan samun rahoton, DPO din Obalende, SP Omoniji Sunday ya tura jami'ai inda abun ya faru kuma an mika gawar zuwa ma'adanar gawawwakin babban asibitin Ijebu Ode. An kuma baza jami'an don damko wanda ake zargin sakamakon guduwar da yayi." ya ce. "Kokarin jami'an ya yi amfani a ranar 1 ga watan Maris na 2020 yayin da wanda ake zargin ke kokarin hawa mota don barin garin."

Ya ce. Bayan damke shi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na halaka dattijon ne bayan ya zargesa da satar masa waya. A yanzu dai, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin mika lamarin ga sashi na musamman na binciken laifukan kisan kai, don bincike don gurfanarwa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN