"Abin kunya" Sheikh Abubakar Giro ya tsaga wa Gwamnatin jihar Kebbi gaskiya mai zafi

Shahararren Malamin addinin Musulunci, kuma babban jigo a kungiyar Jama'atu Izalatu bid'ah wa ika,matus sunnah JIBWIS, Sheikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu, ya ce abin kunya ne a ce babu Ma'aikata ko mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawara watau S.A kan harkokin addinin Musulunci a fadin jihar.

Sheikh Giro ya ce " Ace bamu da ma'aikatan addinin Musulunci a jihar Kebbi wannan abin kunya ne, ina son Gwamna ya san ni na fadi wannan. Don na gaya mashi gaskiya. Bai dace ba a ce akwai Ministry na kula da aikin gona, adviser siyasa, adviser kiwon lafiya, amma ina adviser na addini?

Kuma mu bamu ce wa Gwamna dole sai ya ba wane ba, a a, ya yi tunani duk wanda yake so ya dai ba wanda ya dace. Amma a bar jihar Kebbi babu adviser na addini, Kebbi ta yi kunya, kuma dukkanmu bamu ji dadi ba. Kuma muna fata Gwamnati ta yi gyara.Ya yi wa  girman Allah ya gyara, Ya yi wa  girman Allah ya gyara, ya mutunta gefen addini sama da komai, wanna shi ne rokon mu kuma Allah ya sa a saurari kiran mu.

Kuma Gwamnati ta sani, mun jawo mu kusa da ita ne fa domin mu ba ta shawarwari, in ba don mu ba Gwamnati shawara ba, ai mun lalace akan mu bayan Gwamnati. Ba lalurar mu bane, siyasa ba aikin mu bane, don haka mu za mu ba hukuma shawara, ta yi abin da ya kamata.

Amma abin kunya ne jihar Kebbi ga Mai Martaba Sarkin Gwandu zaune, Gwamnan mu Musulmi, kuma ace bamu da adviser na addini, Ministry na addini babu, balle su ba da shawarwari kan addini, balle su dora mutane ga abin da ya kamata, wannan bai kamata ba"  inji Sheikh Abubakar Giro Argungu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari