Lauyan mai suna Dinesh Parate, yana fuskantar matakin ladabtarwa da tuhumar cin mutuncin Kotu da yin katsalandan ga Kotu bayan ya aikata marin.
Majiyar isyaku.com ya ce, Lauyan ya bi Alkalin ne zuwa na'ura mai zirga-zirga da hawa da sauka na jama'a a ginin Kotun a hawa na 7, a gundumar Nagpur bayan zaman Kotun da rana, a ranar Laraba, inda ya waska ma Alkali K R Deshpande mari a kumatunsa na dama, daga bisani Lauyan ya yi kokarin ya gudu amma aka kamashi.
'Yansanda sun ce Lauyan bai ji dadin yadda Alkalin ya yanke hukunci kan shari'a da ya yi ba ,shi ya sa ya dauki wannan mataki na mari domin ransa ya baci.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari