Yadda wani saurayi ya gamu da tonon asirin Duniya

Jakar magori a yau ta dira jihar Lagos inda ta samo mana labarin yadda wani saurayi ya sace wayar salula na wata budurwa yayin da suke cikin wata motar bus a Oshodi. Bayan wannan saurayi ya saci wayar budurwar, sai ya yi sauri ya saka a cikin Pant nashi domin kada a kula, bai kashe wayar ba.

Can budurwa ta lalabo waya amma bata gani ba, sakamokon haka sai aka bukaci kowa ya tsaya cak domin a caje shi, amma sai wani fasinja ya ce a fara kiran lambar wayar ko da wayar ta fadi ta shige wani guri a cikin motar.

Jama'a suka yarda da wannan shawara, sai wani ya tambaye budurwa lambar wayarta, kuma sai ya kira lambar, abin kunya !... sai ga waya na kara a cikin Pant na wannan saurayi. Sauran bayani ya rage ga mai karatu. Daga karshe dai an mika barawon waya ga 'yansanda kamar yadda ka gani a hoto a saman wannan labari.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN