Tsige Sarki Sanusi, kamashi, fitar da shi daga fadar Sarki da jihar Kano gaba daya

Ba bata lokaci: An fitar da tubabben Sarkin Kano daga fadar sarki, zai bar Kano Read more: https://hausa.legit.ng/
Rahotun Legit Hausa

Jami'an tsaro sun kama Sarki Sanusi  

Rahotanni da muke samu a yanzu sun kawo cewa a ranar Litinin, 9 ga watan Maris, jami’an tsaro sun kama tsigaggen Sarkin Kano sannan suka dauke shi daga birnin mai tsohon tarihi bayan tsaurara matakan tsaro. 

An tattaro cewa jami’an tsaron sun yi jahar Nasarawa da shi inda zai kare rayuwarsa a mafakar. Kafin a dauke shi, an rufe Sanusi a masarautar inda jami’an tsaro na DSS, yan sanda da sojoji suka hana shiga da kuma fita. 

An kama shi ne bayan jami’an tsaro sun rufe fadar. Wata majiya daga gidan gwamnati ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda ya jagoranci taron gaggawa na masu ruwa da tsaki zai sanar da sabon sarki a kowani lokaci. A safiyar yau Litinin, 9 ga watan Maris ne dai majalisar dokokin jahar ta Kano ta amince da sauke Sanusi daga kujerar sarauta.


An fitar da tubabben Sarkin Kano daga fadar sarki, zai bar Kano 

Tsohon sarkin Kano da gwamnatin ta tube wa rawani a ranar Litinin, Muhammadu Sanusi II, zai bar jihar Kano a yau, Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa cewa masanarta ta tabbatar mata. Kazalika, majiyar ta sanar da Daily Trust cewa tuni gungun jami'an tsaro suka kwace iko da fadar domin fitar da Sanusi daga jihar Kano.

Sai dai, a wani labarin da Legit.ng ta samu daga shafin jaridar BBC Hausa na nuni da cewa tuni an fitar da Sanusi daga fadar Kano, kuma za a raka shi ya hau jirgi don barin Kano. Kwamishinan yada labaran jihar Kano, Muhammde Garba, ya tabbatar wa da BBC cewa an bawa Sanusi tsaro, a saboda haka ba ya fuskantar wata barazana a yayin da za a raka wurin da zai zame masa mafaka.

Wata majiya mai kusanci da fadar Kano ta sanar da Daily Trust cewa Sanusi zai tashi zuwa Abuja a yau, Litinin Rundunar jami'an tsaro a ranar Litinin ta tsinkayi fadar Sarkin Kano da ke jihar Kano. Wannan ya biyo bayan tumbuke Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da ofishin gwamnan jihar yayi.

Rundunar jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda da jami'an NSCDC ne suka mamaye harabar fadar, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito. Gwamnati ta jibge jami'an tsaro a fadar ne gabanin sanar da sabon sarkin da zai maye gurbin sarki Sanusi, kamar yadda jawabin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bayan sanar da tsige Sanusi.

Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani

Ganduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani Read more: https://hausa.legit.ng/1309623-yanzu-yanzu-ganduje-ya-kwancewa-sarkin-kano-rawani.htmlGanduje ya kwancewa Sarkin Kano rawani
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020.

Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II." Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa. Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar.

Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati. Yace: "Ya kamata a sani cewa a lokuta da dama, Malam Muhammadu Sanusi II ya kasance mai karya sashe na 3 na dokar masarautar kuma idan aka cigaba da zuba masa ido, zai lalata mutuncin masarautar."

Mun kawo muku rahoton cewa Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun barke da fada da safen nan yayinda kwamitin binciken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin gabatar da rahoton kwance masa rawani.

Daily Nigerian ta ruwaito. Rikicin ya fara ne yayinda mataimakin kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya nemi izinin gabatar da rahoton yau. Amma yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP suka ce a dakatad da gabatar da rahoton binciken sai ranar Talata domin kara dubi cikin rahoton; kawai sai rikici ya barke wanda ya kai ga dan majalisa mai wakiltar Warawa ya dauke sandar majalisa. Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akwai alamun cewa yau za'a kwancewa sarki Sanusi rawani ko ta rahoton majalisar, ko kuma ta hukumar yaki da rashawar jihar.

 Nan ba da dadewa ba zamu nada sabon sarki - Ganduje

Bayan sauke Muhammadu Sanusi II a daga saurautar sarkin Kano, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga al'ummar jihar su kwantar da hakunlansu kuma za'a nada sabon sarki nan ba da dadewa ba. Sakataren yada labaran gwamna Ganduje, Abba Anwar, yace: "Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga al'umma sun kasance masu bin doka kuma su kwantar da hankulansu.

Za'a nada sabon sarkin Kano ba da dadewa ba." Mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020. Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II." Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa.

Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar. Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati. Yace: "Ya kamata a sani cewa a lokuta da dama, Malam Muhammadu Sanusi II ya kasance mai karya sashe na 3 na dokar masarautar kuma idan aka cigaba da zuba masa ido, zai lalata mutuncin masarautar "An tunbukeshi ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar"

Jerin wadanda ake tunanin za su samu sabuwar sarautar Birnin Kano

Bayan an tunbuke Muhammadu Sanusi II daga sarautar Birnin Kano, an fara magana game da wanda ake sa ran zai karbi wannan babbar kujera na gidan Dabo an jima. BBC Hausa sun kawo jerin wasu manyan masu rike da sarauta uku a Kano da ake tunanin a cikinsu ne Masu nada sarki da gwamnatin Kano za su zabi Magajin Sanusi II.

1. Abbas Sanusi (Galadiman Kano) 

Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya na cikin wadanda ake ganin zai iya zama sabon Sarkin Birni. Galadiman Birnin shi ne wanda ya fi kowa matsayi yanzu a fadar Sarki bayan Waziri. Abbas Sanusi Mahaifi ne a wajen Muhammadu Sanusi II, kuma ya na cikin manyan ‘Ya ‘yan Sarki Sanusi I wanda ya fara nada shi Hakimi a Ungogo kuma Sarkin-Dawakin Tsakar Gida a 1959. Bayan nan Abbas Sanusi ya rike sarautar Dan Iyan Kano da Wamban

2. Nasiru Ado Bayero (Ciroman Kano)

Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda shi ne ‘Dan Sarki Ado Bayero na uku a Duniya ya na cikin wadanda ake yi wa hangen wannan gadon sarauta. Nasiru Ado shi ne Hakimin Nasarawa a Birni.Sarki Sanusi II ne ya nada Amininsa kuma ‘Dan Marigayi Sarki Bayero a matsayin Ciroman Kano. Nasiru Bayero ya karbi rawanin ‘Danuwansa Sanusi Bayero wanda ya ki yi wa Sanusi mubaya’a. Nasiru Bayero babban ‘Dan kasuwa ne kuma Attajiri wanda ya ke da ilmin boko na zamani wayewar Duniya. Kafin yanzu ya rike Turakin Kano. Ciroma ya yi aiki har a kasar Ingila.

3. Aminu Ado Bayero (Sarkin Bichi)

Akwai yiwuwar Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da Mai martaba Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Birni. Aminu Ado shi ne ‘Dan Marigayi Ado da ke rike da kasa a yanzu. Tsohon Wamban na kasar Kano ya san gidan sarautar da ya tashi. Kafin yanzu ya rike Sarkin Dawakin tsakar gida. Bayan rasuwar Tijjani Baba Hashim, Sanusi II ya nada shi sabon Wambai.


Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020. Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II." Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa. Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar. Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati. Yace: "Ya kamata a sani cewa a lokuta da dama, Malam Muhammadu Sanusi II ya kasance mai karya sashe na 3 na dokar masarautar kuma idan aka cigaba da zuba masa ido, zai lalata mutuncin masarautar." Mun kawo muku rahoton cewa Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun barke da fada da safen nan yayinda kwamitin binciken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin gabatar da rahoton kwance masa rawani. Daily Nigerian ta ruwaito. Rikicin ya fara ne yayinda mataimakin kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya nemi izinin gabatar da rahoton yau. Amma yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP suka ce a dakatad da gabatar da rahoton binciken sai ranar Talata domin kara dubi cikin rahoton; kawai sai rikici ya barke wanda ya kai ga dan majalisa mai wakiltar Warawa ya dauke sandar majalisa. Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akwai alamun cewa yau za'a kwancewa sarki Sanusi rawani ko ta rahoton majalisar, ko kuma ta hukumar yaki da rashawar jihar. Read more: https://hausa.legit.ng/1309623-yanzu-yanzu-ganduje-ya-kwancewa-sarkin-kano-rawani.html
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN