Dalla dalla: Gwamna Bagudu ya lissafa yadda ake kashe dukiyar jihar Kebbi kowane wata

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana dalla dalla yadda Gwamnatin jihar Kebbi ke kashe kason kudin da take samu na kimanin N3,9b daga Gwamnatin tarayya.

Gwamna Bagudu ya yi wannan bayani ne a garin Birnin kebbi ranar Lahadi, wajen taron Kaddamarwar gidanauniyan neman taimakon kudi da kayan aiki, da hukumar Hisbah na jihar Kebbi ta gudanar a dakin taro na shugaban kasa.

Bagudu ya ce " Muna kashe kusan naira biliyan biyu (N2b) wajen biyan albashin Ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi tare da Pansho na tsofaffin Ma'aikata.

Muna raba akalla Naira Miliyan dari bakwai (700m) ko fiye ga Ma'aikatun Gwamnati.

Muna biyan Naira Miliyan sittin wajen tafiyar da harkokin Majalisar dokoki na jihar Kebbi kowane wata.

Muna ciyar da daliban makarantu a kan Naira Miliyan dari uku (N300m)

Muna ba Asibitoci abin da ya sauwaka, wasu mukan basu N300,000  ko N400,000. Wasu kuwa basa kaiwa haka".

Gwamna Atiku Bagudu ya ce, " Kashi 96% na kudin shiga na jihar Kebbi, ana samu ne daga Gwamnatin tarayya, wanda kimanin Naira Biliyan uku da Miliyan dubu dari tara da hamsin (N3.95b) ne kason jihar Kebbi. Ba a taba rashin biyan albashin Ma'aikata, ko Pansho na tsofaffin Ma'aikata ba, tun da na zama Gwamnan jihar Kebbi.

Gratuti ne ake dan samun jinkiri wajen biyansa, domin Sakataren dindin dim, ko Alkalai da sauran manyan Ma'aikatan Gwamnati, sukan karbi kusan Miliyan 13 zuwa 20 a zaman Gratuti, wanda sau daya ake biya bayan mutum ya yi ritaya daga aikin Gwamnati.

Ragowar kilan N1m ko 2m muke biyan kwangiloli, taimakon kungiyoyin addini da sauransu.

A jawo hankalinmu inda kuskure yake, haka muke tafiyar da abubuwa, dole a yi amfani da dukiyar Gwamnati wajen taimaka wa kowa, ba na Ma'aikata bane, na al'umma ne" inji Gwamna Bagudu.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post