Yadda shugaba Buhari ya hana Gwamna Ganduje tsige Sarki Sanusi shekaru uku da suka gabata

Rahotun Legit Hausa
Duk da yunkurin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na sulhunta Abdullahi Umar Ganduje da Muhammadu Sanusi II, a karshe dole wannan rikici ya ci Mai martaba.
Kamar yadda mu ka samu wani dogon rahoto daga Jaridar Daily Trust mun ji cewa, gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fara yunkurin tsige Muhammadu Sanusi II ne tun 2017.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Buhari ya yi bakin kokarinsa na shawo kan sabanin da aka samu tsakanin Sarkin Kano da kuma Gwamnatin jihar ta Kano.
Rigima ta fara shiga tsakanin shugabannin biyu ne bayan da Muhammadu Sanusi II ya fito gaban Duniya ya na sukar aikin jirgin kasan da gwamnatin Ganduje ta yi yunkurin kawowa.
Tun daga wannan lokaci gwamna Abdullhi Ganduje ya shiga shirin tunbuke Sanusi II, ya kuma sanar da shugaban kasa Buhari, wanda shi kuma ya nuna masa cewa yin hakan bai dace ba.
A Nuwamban 2017, fadar shugaban kasa ta rubuta takarda, ta na bukatar ayi sulhu tsakanin Sarki a wancan lokaci da gwamnatin Ganduje. A dalilin wannan aka nada wani kwamitin sasanci.
Rahotannin sun bayyana cewa abin da ya batawa Mai girma Abdullahi Ganduje rai shi ne zargin shigar Muhammadu Sanusi II cikin harkar siyasa inda ya yi wa tazarcensa adawa a 2019.
Kwamishinan yada labarai na Kano, Malam Muhammad Garba, ya tabbatar da cewa babu hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a game da tsige Muhammadu Sanusi daga kan karaga.
A cewar Kwamishinan, gwamnan Kano ya dauki wannan mataki ne bayan duk wani yunkuri na yin sulhu ya ci tura. Muhammad Garba ya ce tun 2017 aka soma wannan mummunan rikici.
Gwamnatin Kano ta zargi tsohon Sarkin da rashin ba ta goyon baya a tsare-tsaren da ta kawo na inganta rayuwar jama’a. Garba ya ce babu gwamnan da zai yi irin hakurin da Ganduje ya yi.
DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN