Matata ta gujeni lokacin da aka koreni daga aiki, yanzu tana son dawowa don na sami kudi, miye shawararku

Rahotun Legit Hausa

Wani mutumi mai suna Jimoh Kazeem yana neman shawara a wajen al'umma akan wata matsala da take damunsa matuka

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa matarsa da suka yi aure shekarar da ta gabata, watanni biyu da suka wuce ta gudu ta barshi, inda ta ce baza ta iya zama da mutum marar aikin yi ba, bayan haka kuma ta kwashe komai na gidan, inda ta kai ga ya koma rokar wasu abubuwan a wajen makota da abokanan sa.


Sai dai kuma cikin ikon Allah, bayan watanni shida da faruwar wannan lamari wajen da yake aikin suka kira shi suna bashi hakuri akan cewa kuskurene ya sanya suka kore shi ba, inda har suka bashi kyautar naira miliyan sha biyar a matsayin toshiyar baki.

"Shekaruna 26, amaryata kuma shekarunta 28, mun yi aure shekarar da ta gabata, amma bayan auren mu sai na rasa aikina hakan ya saka matata ta gudu ta barni, bayan mako daya ta dawo ta kwashe komai na gidan, na cigaba da rayuwa haka ni daya, ina bacci a kasa na tsawon watanni shida.

"Kawai watarana sai na samun kiran waya daga wajen dana yi aiki, aka bayyana mini cewa kuskurene ya sanya aka kore ni da laifin cewa na saci kudi, yanzu an kama barawon, saboda haka za a mayar dani bakin aiki, sannan kamfanin zai biyani duka albashin dana rasa a baya da kuma alawus.

"Lokacin dana koma wajen aiki an bani kudi naira miliyan goma sha biyar (N15,000,000) a matsayin albashi da alawus dina. Yanzu matsalar shine matata na son ta dawo bayan taji cewa na samu wannan kudi kuma na koma aiki. "Shin wace shawara zaku bani, na saketa ne ko kuma na dawo da ita?

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN