Rahotun Legit Hausa
Antoni janar din kasar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce bashi da hadi da sauke rawanin tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da kuma mayar dashi zuwa jihar Nasarawa. Malami ya sanar da hakan ne a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Lahadi ta hannu Dr Umar Gwandu, mataimaki na musamman gare shi ta fannin yada labarai.
“Maganar sauke rawanin basaraken an mika ta gaban shari’a kuma ana duba ta. Don haka ba zanyi tsokaci a kan maganar da ke gaban kotu ba.”
Sanusi ya yi ikirarin cewa Antoni janar din jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar din kasa ne suka ba hukumar jami’an tsaro ta fararen kaya da ‘yan sanda umarnin tsaresa. Kamfani Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, tubabben sarkin Kano din a ranar Alhamis ya maka sifeta janar din ‘yan sanda Najeriya,
Mohammed Adamu, Darakta janar din DSS, Yusuf Bichi, kwamishinan shari'ar jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan zarginsu da tsaresa .
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN