• Labaran yau


  Sakamakon gwajin cutar covid19 na tsohon Sarki Sanusi da matansa ya fito

  Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi tare da matansa basu dauke da cutar coronavirus.Wannan ya biyo bayan sakamakon wani gwaji da aka yi wa Sarkin tare da matansa ne kamar yadda 'dan Sarkin  Ashraf ya ambato yau da rana.

  Ashraf ya ce iyalin Sarkin sun sami koke koke bayan wasu daga cikin wadanda suka yi mu'amala da Sarkin sun kamu da cutar.

  'Yan Najeriya sun damu da halin lafiyar Sanusi ne bayan Gwamna El-rufai ya kamu da cutar, kuma ya ziyarci Sanusi a jihar Nassarawa.

  Asharaf ya ce " Muna godiya ga dukkannin wadanda suka damu. Mahaifina ya yi gwajin cutar coronavirus amma sakamako ya bayya cewa baya dauke da cutar".

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sakamakon gwajin cutar covid19 na tsohon Sarki Sanusi da matansa ya fito Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama