Type Here to Get Search Results !

Main event

Kungiyar Musulunci ta saka baki cikin rikicin Sanusi da hukumar rashawa ta Kano

Rahotun Legit Hausa

Wata kungiyar Musulunci mai suna Muslim Youth League (MYL) ta yi kira ga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano Muhammad Sanusi II game da zargin rashawa da ake masa.

Kungiyar ta zargi Sarkin da sayar da wasu filaye ba bisa ka'ida ba mallakar masarautar da kudin su ya kai naira biliyan 2 kuma da karkatar da kudaden ta hanyar amfani da wasu kamfanoni domin amfanin kansa.

A cikin sakon da ta aike wa manema labarai a ranar Asabar 7 ga watan Maris, kungiyar ta nuna rashin jin dadin ta kan yadda zargin da ake masa ke shafar al'ummar musulmi a kasar. Idan ba a manta ba,

Kungiyar Yaki da Rashawa da sauraron kararrakin al'umma ta aike da gayyata ga Sarkin domin ya gurfana gabanta a ranar 9 ga watan Maris na 2020 ya amsa tambayoyi.

Sai dai Sarki Sanusi ya shigar da bukatarsa a babban kotun jihar Kano domin neman kotun ta tana hukumar ta rashawar bincikarsa. A cewar kungiyar musuluncin, "Sarkin ya dena labewa ya tafi ya wanke sunansa.

Ya dena gudu kamar kazar da ba ta da kai ya tafi ya fuskanci zargin da ake masa. "Ya dena tursasa hukumar rashawar ta bayyana sunayen wadanda suka tsegunta musu bayanan sirri domin hakan ka iya cikas ga binciken.

"Sarkin ne ya zargi tsohon shugaban kasar mu da cin hanci yanzu shima ga shi an same shi da karkatar da kudaden al'umma. Ya rufa wa kansa asiri.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies