Rahotun Jaridar Aminiya
A daren Juma’ar da ta gabata ne wasu da ake zargin ‘yan
kungiyar asiri ne suka dirar wa kasuwar Lafenwa a Abeokuta inda suka
kashe wani mahauci mai suna Muhammad Tasi’u da ke sayar da balangu suka
sassare shi, suka kwace masa kudi da wayar salula suka kwashi naman da
yake sayarwa suka bar shi cikin jini lamarin da ya yi ajalinsa.
Sarkin Hausawa Abeokuta ya shaidawa Aminiya cewa, baya ga mahaucin
‘yan kungiyar asiri sun kashe karin mutum biyu a kasuwar ta Lafenwa inda
suka jikkata wasu da dama, ” Sun zo shigewa ne cikin zuga domin suna da
dimbin yawa cikin tsakiyar dare inda suka yi ta sare saren kan mai uwa
da wabi, sun isa wajen mai sayar da nama, kamar za su saya sai suka
haushi da duka da sara sun kwashe masa kudi da kayan cinikinsa da
wayoyin salularsa suka tafi suka bar shi cikin jini.”
Sarkin Hausawan ya ce, an garzaya da mamacin asibiti inda aka ki
karbarsa kafin daga bisani ya rasu, “Bayan mahaucin sun kashe wasu
Yarbawa biyu a kasuwar.” in ji shi.
Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar
Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, inda ya tabbatar da abkuwar lamarin, ya ce an
kame shugaban kungiyar asirin, kana rundunar na ci gaba da farautar
ragowar, ya ce zuwa yanzu zai iya tabbatar da mutuwar mutum daya ne,
“Shi yasa jami’an mu a ko wani lokaci muke yaki da aikace-aikacen
kungiyar asiri domin matsalar ba wai a tsakaninsu take tsayawa ba, tana
shafar wadanda ba suji ba, basu gani ba.” in ji shi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN