Rahotun Legit Hausa
Kotun shari'ar musulunci dake unguwar hausawa filin hockey kano, ta gayyaci shahrarren jarumin fina-finan Hausa wato Kannywood, Haruna Yusuf, wanda aka fi sani da baban chinedu. Kotun ta sammaceshi ne sakamakon maganganun da yayi wadanda a cikinsu yake zargin Ismael Naabba Afakallah da cinye kudaden marayu.
Afakallah ya garzaya zuwa kotun Musulunci domin neman a fito da gaskiyar maganar tsakaninshi da Baban Chinedu. Bayan da kotun ta saurari korafi daga mai kara, sai ta saka ranar 1 ga watan 4 na shekarar 2020 domin fara sauraren shari'ar. Babban Chinedu ya shiga takun tsaka da Afakallahu ne tun lokacin da aka bukaci dukkan jaruman fina-finan Hausa suyi rijista kuma an tantanceshi kafin ya cigaba da harkar fim.
Shi kuma Baban Chinedu ya bayyana a wani sabon bidiyo, inda ya nuna sam babu wannan maganar a tsarin shi, har ya bayyana cewa yana jira yaga wanda zai zo yace mishi yayi rijista kafin ya cigaba da wasan fim. Ga abinda jarumin ya ce a bidiyon:
"Hmmm! na sake dawowa, kuna ganin dan malamanku da bokayenku sunje sunyi muku aiki zan daina magana ne, ko kadan bazan daina magana ba na danje hutun rabin lokaci ne kamar yadda 'yan kwallo suke yi.
"Wai mu zo muyi rijista? Kai ka isa kai din banza kai wanene kai, ka manta lokacin da kace da bakinka ba sai jarumi yayi rijista ba, wato yanzu da yake lokacin siyasa ne, kuna so ku ci kudin mutane kuma ku dinga juya su yadda kuke.
"Mu muna karkashin kungiyar Kannywood ne ba karkashin kungiyar tace fina-finai ba, dama ina so na gargade ka, kana zuwa kana cewa mutane kai ne shugaban 'yan fim, ka daina yiwa mutane karya, saboda muna da shugabannin mu, saboda haka kada ka kara zuwa ka yiwa mutane karya.
"Yanzu kuma kirkiro cewa azo ayi rijista, muna nan muna jira, ni ina jira naga wanda zai kirani a waya yace Baban Chinedu kazo kayi rijista, wannan rainin wayo ne, so kuke ku kashe kungiya kowa ya dawo karkashin ku kenan," in ji babban jarumin barkwanci Baban Chinedu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari