An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota

Rahotun Legit Hausa

‘Yan sandan kasar Italiya sun damke wasu ma’aurata da suke saduwa a cikin mota tare da yin karantsaye ga dokar kebancewa ta coronavirus. Ma’auratan da aka gano mijin dan asalin kasar Egypt ne mai shekaru 23 sai kuma matar ‘yar asalin kasar Tunisia ce mai shekaru 40.

An kama su ne a kan titin Mecenate da ke birnin Milan, inda cutar coronavirus ta fi barkewa. Kamar yadda jaridar Daily Mail UK ta wallafa, wnai dan sanda ne da ke bakin aiki ya kama ma’auratan. Karin rahoto a kan hakan ya bayyana cewa dokar kebancewa da aka saka ta coronavirus ta haramtawa mutane biyu zama a waje daya a cikin mota.

Amma kuma ko a yayin sanar da dokar, ba a tabbatar da cewa za a hukunta ma’aurata ba a kan hakan. Kasar Italiya ta bayyana a cikin daya daga cikin kasashen da mugunyar cutar coronavirus ta addaba a duniya. Hakan kuwa yasa aka rufe kasar don gudun yaduwarta.

‘Yan kasar Italiya na iya fita ne kadai daga gidajensu don siyan abinci ko kuma samun taimakon masana kiwon lafiya. Dan kasar ne kuma mutum na farko da ya shigo Najeriya dauke da muguwar cutar.

Bayan killacesa tare da bashi magani, ya warke daga muguwar cutar. Mutane 3,526 ne na kasar Italiya suka kamu da cutar a cikin kw anakin nan. Hakan yasa masu cutar a kasarr suka ka 31,506. Amma an samu mace-macen mutane 2,503 na jama’a.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN