Tsabar jarabar mijina ko a lokacin da nake jinin al'ada zuwa yake yayi jima'i dani - Matar aure

Rahotun Legit Hausa

A jiya Juma'a ne wani mutumi mai suna Abidemi Dada, ya bayyanawa wata kotun dake Ibadan yadda rayuwar aurensu na shekara 13 ta kasance da matarsa Opeyemi, saboda rashin mutunta juna da kuma matsala wajen jima'i Da yake magana a gaban alkalin kotun, Cif Ademola Odunade, Abidemi ya ce matarshi ba ta bashi damar yin jima'i da ita duk lokacin da ya bukaci haka daga wajenta.

Ya ce yayi abubuwa da dama domin ya burge matar tashi, amma maimakon ta nuna farin ciki sai ta yi kamar ma babu wani abu da ya faru. "Abinda kawai Opeyemi take gayawa mutane shine, bana kula da ita yadda ya kamata, bayan ni ina yin iya bakin kokarina wajen ganin na sanyata farin ciki.

"A duk lokacin dana bukaci kwanciya da ita, sai ta fara yi mini ihu wani lokacin ma ta fara zagina. "Bana mancewa akwai lokacin da Opeyemi take fada mini cewa talaucina shine babban dalilin da yasa bata bin umarnina kuma ta canja mini.

 "Ta sha fada mini cewa tasha tunanin ta kashe ni kawai. "Haka kuma, Opeyemi sai ta dinga bawa 'ya'yanmu gari suna ci, inda ita kuma za ta je ta ci abinda ranta yake so da kudin da nake bata na abincin mu baki daya,"

Abidemi ya ce. Opeyemi wacce take dan taba kasuwanci na tireda ta bayyana cewa ba ta taba yiwa mijinta barazanar za ta kashe shi ba, amma ta ce tabbas yanzu ta daina bari ya kwanta da ita. "Ya mai shari'a Abidemi mutumin banza ne wanda bai dace dani ba. 'Baya so na dauki ciki, amma kuma kullum sai ya dinga kwanciya dani ba tare da kwaroron roba ba.

"Abidemi ya saka na zubar da ciki har sau uku, yanzu haka ina fama da ciwo a gabana saboda wani abu da yake bani na dinga sanyawa a ciki. "Hatta lokacin da nake yin al'ada Abidemi ba kyaleni yake yi ba, sai ya zo yace zai kwanta dani.

"A yadda na duba yanzu haka gabana ya fara lalacewa. Dul lokacin da na dauka ina tare da Abidemi cikin wahala nake," cewar Opeyemi. A nashi bangaren alkalin kotun ya bayyana cewa yana ganin mijin ba zai dauki nauyin kudin maganin matar ba idan har ya raba auren. Hakan ya sanya ya bukaci mijin ya kai matar tashi asibiti domin a duba lafiyarta sannan ya daga sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN